Bola Amed Tinubu cikekken dan Katsina ne, cewar Sarkin Katsina Alhaji Abdlmunini Kabir Usman
Bola Amed Tinubu cikekken dan Katsina ne, cewar Sarkin Katsina Alhaji Abdlmunini Kabir Usman
Alhaji Abdulmunini Kabir Usman Sarkin Katsina ya ayyana tsohon Gwamnan jihar Legas, Bola Ahmed Tinubu a matsayin dan Katsina.
Alhaji Abdulmunini Kabir Usman yayi wannan furucin ne lokacin da ya karbi bakuncin wata tawaga ta ‘yan Arewa, dake goyon bayan takarar Bola Ahmed Tinubu ta Shugabancin Najeriya watau Arewa Organizations Movement For Asiwaju (AROMA).
Bayan haka Sarkin Katsina ya bayyana cewa, fiye da shekaru talatin 30 da suka gabata, tsohon Gwamnan jihar Legas din ya na dan kyakkyawar alaka da masarautar tun lokacin mahaifinsa, Alhaji Muhammadu Kabir Usman don haka zai bayar da dukkan goyon bayan sa ga tafiyar siyasar sa.
Sannan kuma ya kara da cewa, a bisa al’ada baya ganin mutane ranar Juma’a amma sabida alakar tawagar da masarautar ya sa dole ya saurare su.
Tun da farko Shugaban tawagar kuma tsohon Sanatan shiyyar Katsina ta Kudu “Sanata Abu Ibrahim” ya bayyana cewa, sun je wurin Sarkin ne domin girmamawa ga masarautar tare da neman albarkar sa a bisa gurin da suka sa a gaba.