Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa bai aibanta farjin Iyaye Mata ba, Daga Datti Assalafiy
Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa bai aibanta farjin Iyaye Mata ba, Daga Datti Assalafiy
Kamar yadda kuka sani a yanzu haka ana tsaka da cece-kuce kan wata magana da Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya fada akan farjin Mata, wanda har aka sami wata jarumar kannywood ta maida masa martani har ma take cewa.
Wajan da Malam Aminu Ibrahim Daurawa ya aibata tanan uwarsa ta haife shi, kuma a hakan Malamai suke bin Mata.
To a yanzu kuma mun sami wata wallafa daga shafin mai magana Datti Assalafiy inda ya yi wani dogon rubutu kan al’amarin yana mai cewa.
Wata fitsararriya ‘yar Hausa fim taci mutuncin Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa Kano akan wasu kalamai da ya ambata game da farjin mata, har take cewa wai gurin da Malam yake aibatawa ta nan uwarsa ta haifeshi kuma wai a haka Malaman suke bin mata.
Abinda ya faru shine Malam Daurawa wa’azi yayi mai ratsa zuciya akan ita wannan duniya da muke ta rudu a kanta, duniyar da ba abakin komai take ba da har zai sa ka rabu da Allah ka koma kana sabawa Allah saboda duniya ko wani abin jin dadin duniya.
To a haka ne Malam ya zayyano wasu abubuwa guda biyar na jin dadin duniya wanda bai kamata Musulmi ya shagala da su ba wanda asalinsu ba abubuwan burgewa bane, gasu kamar haka.
(1) Turare yana cikin abubuwa masu kamshi da mutum yake so anan duniya , to akwai wata halittar Allah dabba ce kashin dabbar yafi kowani turare kamshi a duniya, “Misk” dabbace, wanda ake kira da “Juda” turaren juda dabba ce, amma idan tayi kashi sai ya zama turare.
(2) Sannan akwai wata dabba tana yin kashi,
kashinta shine abu mafi zaki a duniya wato
kudan zuma.
(3) Yadin da yafi kowani yadi tsada a duniya sakace ta tutsa sunan tsutsar “Tut” tana sakar yadin Harir.
(4) Duk inda kaci abinci mai dadi ka koshi bayan awa 6 ya zama kashi, zakayi kashinsa yazo yana doyi da wari, sannan shi mutum jakace, gangar jikinsa jakace aka saka rai, da zaran an zare ran to sai gangar jikin ta rube, idan ba’a gaggauta yiwa mamaci jana’iza ba sai ya fara wari.
(5) Sannan idan kace mace ce dadin duniya to menene a jikin macen? mafi muni a jikin mace shine gabanta, nan take fitsare take fitar da jini, to menene abin burgewa? shiyasa aka boyeshi ai, inda shi mata suke nuna wa gudu za’ayi, sai fuska itace mafi kyawu a jikin mace, to da kyawun fuskar zata jaka zuwa ga mafi munin abinda ke jikinta, bashi da kyan gani, ta nan take fitsari, kashi da jini da fitar yaro, to me zai ja hankalinka a duniya da har zai rabaka da Allah?.
Malam Aminu Daurawa bai muzanta mata ba, nasiha yayi mai gaba daya, musamman ga mazinata wadanda suka mayar da zina tamkar abin ado suna kaiwa kansu zuwa ga halaka saboda gaban mata.
Kuma ita wannan ‘yar nanayen da taci mutuncin Malam da masu tunani irin nata, gaban matan da ake bayani ai yasha banban da irin nasu gaban na ‘yan duniya wanda bashi da maraba da get free, wanda ba komai a cikinsa sai miyagun infections, kun mayar da gabaku ATM machine, mutane suna sabawa Allah sabida shi.
Imba karwai ba banga wanda zasu yiwa maganar Malam mugun fahimta ba, dole ayi nasiha da sigar data dace k0 da ran kowa zai baci, dole aja hankalin Musulmai su kauracewa karwai, don haka duk wata karwa ta dena karowanci, ta dena raba gabanta, taje tayi aure, fadakarwa da nasiha ba za’a fasa ba har zuwa ranar tashin Alkiyama.