Labarai
Sojojin Kasar Rasha sun kutsa kai birnin Kyiv fadar Gwamnan Ukraine
Sojojin Kasar Rasha sun kutsa kai birnin Kyiv fadar Gwamnan Ukraine
Har yanzu dai sojojin kasar Ukraine na cigaba da karfafa tsaron kyiv a lokacin da sojojin kasar Rasha suke aniyar kutsawa cikin babban birnin Kasar Ukraine.
Advertising
Inda sojojin suke ta tona ramuka tare da toshewa kowace hanya ta yin amfani da motocin taki wanda ake kira da Tanka, kamar yadda BBC Hausa ta ruwaito.
Kamar yadda hukumomin kasar suka bayyana cewa, har yanzu ana cigaba da luguden wuta a wasu birane uku 3 Arewa maso yammacin Kyiv, Bucha, Hostomel, Irpin.
Inda yake cigaba da gwabza gagarumin fada a yankin inda sojojin Rasha suka harba rokoki kan fararen hula a Irpin a lokacin da suke kokarin tserewa, inda suka hallaka wata Mata tare da ‘yayan ta guda biyu sannan kuma suka raunata Matar.
Advertising
Advertising