Tsohon dan wasan kwallon kafar Holland “Clarence Seedorf” ya karbi addinin Musulinci
Tsohon dan wasan kwallon kafar Holland "Clarence Seedorf" ya karbi addinin Musulinci
Shahararran dan wasan kwallon kasa wanda ya jima ana damawa da shi wanda yake buga wasan a kasar “Netherlands” wacce aka fi sani da Holland ” wato “Clarence Seedorf”, ya musulinta kamar yadda Hausaloaded ta ruwaito.
Seedorf wanda yake da shekara 45 da kansa ya sanar da cewa, ya rungumi addinin Musulunci ranar Juma’a ta shafinsa na Instagram, in ji jaridar.
Sanna ya kara da cewa, Ina godiya da sakonnin taya murna da aka yi ta turo min bayan na zamo daya daga cikin al’ummar Musulmi.
Ina matukar farin cikin da kasancewa daya daga cikin ’yan uwa Musulmi na fadin duniya, sannan ina kuma godiya ta musamman ga Sophia wadda na sami zuzzurfan fahimtar Musulunci daga gare ta.
Sannan ya kara da cewa, Ban sauya sunana ba zan cigaba da amfani da sunan da mahaifana suka sanya min, wato Clarence Seedorf, Clarence Seedorf ya buga wa manyan kungiyoyin kwallon kafa na duniya wasa inda ya ja zarensa a tsawon lokaci.
Wanda ya buga wa kungiyoyin kwallon kafa irin su Real Madrid, Ajax, Inter Milan da AC Milan, inda ya yi matukar tashe a wannan lokacin.
Tsohon dan wasan tsakiyan an bayyana cewa, sau hudu yana daga kofin Gasar Zakarun Turai; Ajax, a 1995, sai Real Madrid a 1998 sannan AC Milan a 2003 da kuma 2007.
Bayan haka kuma ya lashe gasar La Liga a 1997 a kungiyar Real Madrid, sannan sau biyu yana lashe gasar Serie A tare da kungiyar AC Milan a 2004 da 2011.