Advertising
Advertising
Labarai

Turkashi: Yan bindiga sun Tasa keyar amarya yayin kaita dakin mijinta.

Wata sabuwar Amarya ta fada hannun ‘yan bindiga akan hanyar kai ta zuwa gidan mijin ta a jihar Neja a Nigeria.

Advertising

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa ‘yan bindigan sun kawo harin ne lokacin da ‘yan’uwan amaryar su ka dauko ta daga kauyen Allawa a karamar hukumar Shiroro zuwa garin Pandogari, a karamar hukumar Rafi ta jihar Niger.

Yan bindigan waɗanda su ka zo da yawa sun farmake su a hanya, sannan su ka dauke Amaryar da sauran mutanen da ke wajen a cikin wata babbar mota da ake daukar Amare.

Shugaban majalisar matasan Lakpma, Jibrin Abdullahi Allawa, ya bayyana cewa lamarin ya auku ne ranar Juma’a yayin kai amarya dakin mijinata.

Advertising

A cewar wata majiya, ‘yan bindigan wadanda kuma su ka sace shanaye masu yawa sun kai wani harin a kauyen Gyaramiya, har ila yau cikin Shiroro, inda su kayi awon gaba da wasu daga cikin mazaunan kauyen.

Lamarin na zuwa kwanaki ƙadan bayan gwamnatin jihar ta bayar da sanarwar cewa ta samo nasara sosai akan ‘yan bindiga

Ba’a samu jin ta baki jami’an tsaro jihar ba har i zuwa yanzu

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button