Advertising
Advertising
Labarai

An kama Ummi Rahab ta bogi ta handame kudaden wani matashi dan Amerika

An kama Ummi Rahab ta bogi ta handame kudaden wani matashi dan Amerika

Rundunar ‘yan sandan jigar Kano tayi nasarar kama wata sananniyar jarumar wasan hausa nan Ummi Rahab amma ta bogi, tun da fari dai wani mazaunin kasar Amurka dan asalin jihar Kano ya shigar da karar ta a rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta hannun abokin sa kan cewa.

Advertising

Sun hadu da matashiyar da ake amfani da sunan Ummi Rahab a shafin sada zumunta na Facebook, wanda a haka a haka har soyayya ta kullu a tsakanin su wanda har matashin ya kuduri aniyar angwancewa da jarumar a matsayin Ummi Rahan.

Bayan daukar wasu lokatu yana kashe mata makudan kudade ya gano cewa, ashe dai ba ita bace Ummi Rahab ta asalin kawai dai tazo ne domin ta karbe masa ‘yan kudaden sa.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Kamo SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya bayyanawa jaridar Nagarcacciya cewa, daga lokacin da suka sami wannan korafi suka shiga binkice har Allah ya sa suka yi nasarar kamo matashiyar tun ba’a je ko ina ba.

Advertising

Matashiyar da aka kama mai suna Nisaiba Yahaya ‘yar shekara goma sha takwas 18 wanda take zaune a unguwar Hotoro ta tabbatar da cewa, hakika ta bude shafin Facebook da sunan Ummi Rahab wanda hakan ya bata damar yaudarar wannan matashin mazaunin kasar Amurka tare da karbe masa kudade.

Haka zalika SP Kiyawa ya tabbatar da cewa, zasu sanar da ‘yan jarida halin da ake ciki da zarar sun kammala bincike a matakin farko kafin gurfanar da matashiyar a a gaban kuliya domin girbar abin da ta shuka da hannunta.

Zaku iya kallon bidiyon dake kasa domin kuji sauran wasu labaran a ciki.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button