Advertising
Advertising
Uncategory

Duk wata lalacewar da PDP take dashi gwara ita da jam’iyar APC inji Kwankwaso.

Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, yace jam’iyyar APC ce mafi lalacewa cikin jam’iyyun siyasa a wannan lokacin

Advertising

Kwankwaso ya yi wannan furuci ne a jiya Lahadi, yayin taron masu ruwa da tsaki na ɗarikar Kwankwasiyya a gidansa dake Kano.

Tsohon Sanatan ya kuma ce dukda dai itama PDP ɗin ba kanwar lasa bace wajen kama-karya a yanzu, amma dai za a iya cewa gwara-gwara idan a ka kwatanta ta da APC.

Yace wasu sojojin gona ne su ke yin kama-karya a PDP, inda ya koka da cewa duk cancantar mutum da haƙƙin sa, zai iya rasa shi ta dalilin waɗannan sojojin gonar.

Advertising

Kwankwaso ya jadda cewa har yanzu yana cikin jam’iyyar PDP, amma shirye-shirye sunyi nisa a tsakaninsa da jam’iyyar NNPP.

Kwankwaso yace fita daga jam’iyya da komawa ba illa bane, kuma hakan ma shi ne kwarewa a siyasa.

Ya tuna cewa a shekarar 2018 da su ka yi zaben fidda gwani a Fatakwal, wadanda su ka zo na farko, na biyu, na uku da na hudu, duk sunbar PDP sun dawo, “sai kuma wasu tarkace da suka biyo baya, a cewar Kwankwaso.”

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button