Advertising
Advertising
Labarai

Sojojin Nageriya sun yi nasara hallaka ‘yan ta’adda 17 a jihar Borno

Sojojin Nageriya sun yi nasara hallaka 'yan ta'adda 17 a jihar Borno

Yanzu-yanzu muka sami wani kyakkyawan labari kan yadda Sojojin Nageriya suka hallaka wasu ‘yan ta’adda goma sha bakwai 17 a jihar Borno.

Advertising

Mun sami wallafar labarin ne daga shafin Daily Nigerian Hausa dake kan dandalin sada zumunta na Facebook, inda suka wallafa labarin kamar haka.

Rundunar Sojin Kasa ta bayyana cewa, dakarun ta na Operation Hadin Kai OPHK sun hallaka ‘yan kungiyar Boko Haram da ISWAP a Damasak
dake Karamar Hukumar Mobbar a jihar
Borno.

Shugaban Gamayyar ta rundunar ta Hadin Kai dake Arewa maso Gabas mai suna “Christopher Musa” shi ne ya bayyana hakan a wata tattauna wa da ya yi da Kamfanin Daillancin Labarai na Kasa “NAN” a yau Litinin a Maiduguri.

Advertising

Sannan kuma yace, jajurtattun dakarun sun kuma cafke yan ta’adda uku da ran su, inda ya kara da cewa dakarun sun kuma kwace babura da makamai iri-iri a yayin fafatawar da aka yi a jiya Lahadi.

Bayan haka yace, dakarun ne suka rufar wa ‘yan ta’addan da dama lokacin da suka kawo hari kan wani sansani na sojoji dake daura da kofar fita ta Walada da misalin karfe biyu na dare.

Musa ya kara da cewa, da ga bisani ne ‘yan
ta’addan suka hadu da karfin sojin Nijeriya
da suka rika yi musu luquden wuta a fafatawar da aka yi ta tsawon nawanni.

Sannan ya kara da cewa, sojojin sama ma sun
rusa ‘yan ta’addan inda suka datse su sannan
suka ragargaje su.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button