Labarai

Subhanallah: Yadda wani matashi ya haikewa karamar yarinya

Jami’an ‘yan sandan Jihar Gombe sun damke wani matashi a yankin Tumfure ta jahar kan zargin yi wa wata karamar yarinya fyade

Hukumar ‘yan sandan sun damke matashin da ake zargi a ranar 28 ga watan Fabrairun na wannan shekara da muke ciki bayan shigar da kara da iyayen yarinyar da aka sakaya sunanta suka yi

Shugaban ‘yan sandan dake jihar, Ishola Babatunde Babaita ta hannun kakakin ‘yan sandan jihar, SP Mary Obed Malum, tace ‘yan sanda sun kama matashin da ake zargi ne da laifin bin yarinyar har gida ya ci zarafinta.

SP Mary ta ce matashi ya bi sahun yarinyar ne inda bayan ya gano gidansu, daga bisani ya tsallaka katangar gidan ya keta mata haddi.

A cewarta, bayan faruwar lamarin ne jami’an sa-kai suka garzaya da yarinyar zuwa asibitin kwararru da ke jihar don duba lafiyarta.

SP Mary ta ce wanda ake zargin ya amsa laifinsa, inda ta ce nan ba da jimawa ba za a tura shi zuwa kotu don ya fuskanci hukunci daidai da abin da ya aikata.

Kwamishinar ta ja kuma hankali al’umma musamman masu aikata laifuffuka da cewa su shiga taitayinsu, domin ‘yan sanda suna nan za su ci gaba da zakulo ire-irensu daga cikin al’umma don su gaya wa aya zakinta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button