Advertising
Advertising
Labarai

Gwamnatin Benin ta saki Sunday Igoho mai fafutukar kafa kasar Yarbawa a Nageriya

Gwamnatin Benin ta saki Sunday Igoho mai fafutukar kafa kasar Yarbawa a Nageriya

Kamar yadda muka sami labarin cewa, gwamnatin Benin ta saki jagoran masu fafutukar kafa kasar Yarbawa a Nagwriya Sunday Ighoho.

Advertising

An sake Sunday Ighoho ne domin ya sami ganin Likita a asibiti bisa sharadin cewa, ba zai bar asibiti ba ko cotonou sabida wani dalili kamar yadda daya daga cikin Lauyoyin Aliyu ya tabbatar wa da BBC Hausa.

Sannan yace, Farfesa Wole Soyinka ɗaya daga cikin shugabannin Yarbawa ya taimaka akan Sunday Ighoho domin zuwa asibiti, a watan Yulin shekarar 2021 aka kama Sunday Ighoho mai da’awar kafa kasar Yarbawa ta Oduduwa.

Ana tuhumarsa Sunday Igboho ne da laifin shiga kasar ba bisa kan ka’ida ba tare da kokarin tayar da husuma, amma sai ya musanta hakan, Sunday Igboho ya tsere ne daga Najeriya ya tsallaka Benin bayan samamen da ‘yan sanda suka kai gidansa a farkon watan Yulin shekarar 2021, inda aka kashe biyu daga cikin yaransa.

Advertising
Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button