Labarai

Yadda magoya bayan jam’iya APC da PDP suka bawa hamta isaka.

Mabiya bayan jam’iyyun hamayya PDP da APC sun yi wata arangama a yankin Sabon Gida da ke Karamar Hukumar Langtang ta Kudu a Jihar Filato.

Binciken da gidan Aminiya yay Sun gano lamarin ya faru a ranar Asabar lokacin da ake tsaka da bikin samar wa da ’yan kabilar Tarok matsuguni a cikin Jihar.

Wanda lamarin ya faru a kan idonsa mai suna Lanchang Timpil, ya ce fadan da ya rikide ya koma na siyasa a tsakanin matasan yankin, a lokacin da Ubandoma Laven ya halarci taron.

Saidai bayaninsa a wajen taron bai yi wa Honarabul Vincent Bulus Venman, wanda shi ne sabon shugaban Langtang, dadi ba.

Lamarin ya yi sanadin tada tarzoma a tsakanin magoya bayan bangarorin biyu, wanda suka fito daga APC da PDP, wanda hakan ya jikkata mutane da dama.

Kakakin ’yan sandan Jihar, ASP Ubah Gabriel, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya kuma ce tuni rundunarsu ta fara gudanar da bincike don gano hakikanin abin da ya haddasa tarzomar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button