Advertising
Advertising
Labarai

Yadda wani Boka ya rataye kansa a jihar Benue.

Wani Boka da duniya ta yi masa daurin Giro a jihar Benue daga karshe dai ya yanke shawarar ya hallaka kansa ta hanyar rataya kansa, jaridar aminiya ta wallafa.

Advertising

Shahararren Bokan mai kimanin shekara 42 a duniya dai ya rataye kan nasa ne a gundumar Mbakuha da ke Karamar Hukumar Ushongo ta jihar ta Binuwai.

Mutumin wanda aka bayyana sunansa da Terhemen Lorbee dai rahotanni sun ce an shafe kimanin sa’a 24 ana nemansa an rasa ina ya shiga kafin daga bisani a gano gawarsa tana reto a jikin wata bishiya a karshen sarin nan.

Shaidu gani da ido sun ce ko kafin faruwar lamarin, an ga Terhemen ya koma yin wasu bakin al’adu, lamarin da ya sa iyalansa suka fara shiga cikin damuwa

Advertising

Bokan Ya mutu ya bar mata uku da ’ya’ya hudu a wanan Duniya.

Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar SP Catherine Anene, ta tabbatar wa wakilinmu faruwar lamarin ta wayar salula inda yace suna cigaba da bincike.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button