Advertising
Advertising
Labaran Kannywood

Zazzafan martanin Ali Nuhu ga jaruma Nafisa Ishak kan munanan kalaman da ta fada ga Sheikh Aminu Daurawa

Jarumi kuma Darakta a masana’antar kannywood wanda ake masa lakabi da sarki wato Ali Nuhu, ya yi martani kan jaruma Nafisa Ishak dalilin cin mutuncin da ta yiwa Malamin addini Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa.

Advertising

Inda yake fadin cewa, wata jaruma mai suna Nafisa Ishak ta futo tana maganganun da basu bace ba ga babban shehin malami Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, kan wani fai-fai bidiyo inda malam yake cewa.

babu abu mafi muni da kazanta a jikin mata kamar Farjin su, domin a nan ne su ke fitsari, jinin al’ada, da kuma haihuwa.

Malamin ya ce “saboda munin sa ne ya sa aka rufe shi, domin da mata za su yi yawo tsirara da gudun su za a yi saboda zai zama abin tsoro saboda munin sa.

Advertising

Wanda malamin yayi wannan maganganu ne saboda nuna ga masu zinace zinace amma ita wanna jarumar ta fito gaba gadi tana ashariya ga shehin malamin.

Shine jarumi kuma darakta Ali Nuhu yayi martani kamar haka, duk Wanda Ya San Martabar Addini Ba Zai Zagi Malaman Addini Ba.

Saboda Malamai Sune Suke Koya Mana Bin Allah Da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Sallam.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button