Babu wanda ya tilastawa wadanda ake zargi da kisan Hanifa su amsa laifin ba, a cewar Kotu
Babbar Kotun Jiha mai lamba 5 karkashin
Mai Shari’a Usman Na abba ta yanke hukunci
cewa, ikirarin da wadanda ake zargi da
kisan Hanifa Abubakar suka yi cewa jami’an
tsaro ne suka azabtar da su shi ya sa suka amsa laifin, ba gaskiya ba ne.
A lokacin da yake yanke kwarya-kwaryan hukunci akan hakan a yau Laraba alkalin kotun Mai Shari’a Usman Na-abba yace, bayanan da shaidu suka bayar sun nuna cewa Abdulmalik Tanko babban wanda ake zargi da kisan Hanifa, da Hashimu Isyaku wanda ake zargi da sa hannu a kisan, ba tilasta musu aka yi ba.
A cewar Na-abba, shaidun wadanda sune jami’an da suka yi bincike akan laifin, sun yi wa Tanko da Isyaku tambayoyi ne a cikin ofisoshi kuma da mutane a cikin ofishin.
Ya kara da cewa, babu wata hujja da Abdulmalik Tanko ya bayar ta cewa an azabtar da shi inda yace, ya gaza fadin sunan dan sandan da yace ya mishi azaba, ya kuma kasa fadin sunan
na’urar da yace an rika dana masa a jikin sa.
A bisa haka ne Na Abba yace, dukkan su wadanda ake zargin har da Fatima Jibrin wacce ita dama ba ta de an dake ta ba, amma dai tace an tsorata ta basu da hujjar cewa tilasta musu aka yi su amsa laifin su.