Labaran Kannywood
Duk Ikancin da ake cewa inayi Banyi shirkaba ai cewar Umma Shehu.
Duk Ayyukan Zunuban Da Nake yi Ba Na Yin Shirka, Cewar Jarumar Finafinan Hausa, Umma Shehu
Advertising
Fitacciyar tauraruwar finafinafinan Hausa, Umma Shehu ta ce ta bar masu zaginta da Allah domin kuwa shi ne zai saka mata.
Ta bayyana haka ne a hira da ta yi da majiyar RARIYA, BBC Hausa domin yin raddi ga masu zaginta bisa zargin tana aikata ba daidai ba.
Ta ce a matsayinta na Musulma, tana yi wa Allah laifi kuma ta san zai gafarta mata amma duk da irin laifukan da take yi masa “ba na yin shirka.”
Tauraruwar ta ce ya kamata masu ganin ta aikata ba daidai ba su rika jan hankalinta ba kawai su rika zaginta ba.
A cewarta masu zaginta na kallo za ta shiga aljannah ta bar su suna dakon zunuban da suka dauka saboda zaginta.
Advertising
Daga Jamilu Dabawa
Advertising