Advertising
Advertising
Labaran Kannywood

Lokacin da wasu jarumai ke kokarin yin Aure mun samu labarin mutuwar Aure Zara Daimond

Labarin da muke samu shine fitacciyar jarumar da tayi aure watanni shida zuwa bakwai da suka wuce wato Zahar Diamond, ita ma tabi sahun su Rahama Hassan, Maryam ceeter, Hafsat shehu da sauran su da sukayi auren sirri kuma suka fito daga baya.

Advertising

Wanda cikin wayannan zamu iya cewa Rahama Hassan ce Auren ta yayi karko da har ya haura shekaru 5 amma wuce yan watanni cikin hukuncin Allah ake ganin su sun fito.

Da fari dai tsawon wani lokaci kenan Zahra Diamond ta bude shafukan sada zumunta na Instagram da TikTok tana wallafa yan abubuwanta na nishadi saidai a kwanakinnan ne abubuwan suka chanza salo inda take wasu Bidiyon ma babu dankwali tana wasu raye raye.

Kasancewar an san jarumar ta dauki mataki na daina amfani da duk shafukan sada zumunta kafin Auren ta hakan yasa alamomin tambaya kan kasan tuwar Auren nata domin abin da mamaki a farkon aure ta daina wallafa koda hoto asali ma ta goge dukkan shafukan ta hatta masu shafukan masoya wato fans page sai da ta roka su goge hotunan ta amma Ganta ta bude shafin tiktok tana tikar rawa daga baya.

Advertising

Mun fara bincike kan lamarin inda wata majiya ta tabbatar mana da jarumar Auren ta ya dan kwana biyu da mutuwa kawai dai bata bayyana bane wanda hakan yasa muka tuntubi wani producer dake da alaka da jarumar mai suna Sunusi Multimedia da zummar ya bamu number koya hada mu da ita.

Saidai jarumar ta bada sako a gayan mana cewa a sanda ta tashi Auren ta ba dan jaridar da ta gaya wa daquada bata ga dalilin da zaisa yanzu a dame ta auren ta ya mutu ko baimutu ba.

https://www.instagram.com/tv/Ca5OzIVjQUX/?utm_medium=copy_link

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button