Wata yarinya mai shekara 16 mai suna Hamida ‘yar Jihar Kano ta fada Rijiya ta Mutu
Wata yarinya mai shekara 16 mai suna Hamida 'yar Jihar Kano ta fada Rijiya ta Mutu
Wata yarinya yar shekara 16, Hamida Bawale
ta rasu bayan ta fada rijiya a Kofar Fada Gidan Sarki a Karamar Hukumar Karaye da ke Jihar Kano a jiya Talata.
Kakakin Hukumar Kwana-kwana ta Kano, Saminu Abdullahi ne ya baiyana haka a wata sanarwa da ya fitar a jiyan.
Ya ce lamarin ya faru da yammacin ranar Talata, bayan da Hukumar ta karbi kiran gaggawa da ga ofishin Hukumar Kare Farar hula, NSCDC, reshen Karaye da misalin karfe 4:58.
A cewar Abdullahi, da ga karbar rahoton, sai
hukumar ta yi maza ta tura jami’an ta na bangaren bada agaji, inda su ka isa wajen da
misalin karfe 5:04 na yamma.
Da zuwan su, inji Abdullahi, sai su ka dauko
Hamida, amma tuni rai ya yi halin sa, inda su ka mika gawar ta ta zuwa ga yayanta, Abdullahi Bawale.
Kakin ya kara da cewa marigayiyar ta gamu da ajalin ta ne bayan da ta je debo ruwa a rijiyar shine ta fada ciki, sai dai kuma sanarwar tace