Advertising
Advertising
Labarai

Gwamnatin jihar Bauchi zata aurar da tubabbun Mata Karuwai a kalla guda 100 bayan an koya musu sana’o’i

Gwamnatin jihar Bauchi zata aurar da tubabbun Mata Karuwai a kalla guda 100 bayan an koya musu sana'o'i

A wani labari da muka samu ayanzu kan cewa, Gwamnatin jihar Bauchi za ta aurar da tubabbun karuwai akalla guda dari 100 daga kananan hukumomi ashirin 20 dake jihar, amma sai an kammala koyar dasu sana’o’in dogaro da kai daban-daban.

Advertising

Sai dai wadanda suka tuba suka watsar da sana’ar ta karuwanci suka mika kansu ga Hukumar Hisba, su kadai zasu ci gajiyar wannan shiri da taimako da za’a muau.

Kamar yadda Muryoyi ta ruwaito cewa, a ranar Talata Gwamnatin Bauchi ta yi wani shiri na koyar da sana’o’in hannu ga tubabbun karuwan jihar a kalla guda dari biyar da saba’in da biyar 575.

Sana’o’i da ake koyawa karuwan tare da hadin guiwa da hukumar samar da ayyukan yi ta kasa NDE, sun hada da harkokin kasuwanci, Ilimin sarrafa kwamfuta, Gyaran kai, kitso, saka da kuma Dinki.

Advertising

Sauran Sana’o’i da za’a cigaba da koyawa karuwan sun hada da Kwalliya, sana’ar hada abinci, kiwon kaji, kiwon kifi, hada takalma da jakka da dai sauransu.

Sannan kuma Hukumar ta yabawa karuwan da suka mika wuya daga wannan kazamar rayuwa ta bin maza sa sukw, wacce ke da hadarin gaske Duniya da Lahira.

Gwamnatin Bauchi ta kara da cewa, zata dauki dawainiyar aurar da tubabbun mata karuwan da zaran an kammala koyar dasu sana’o’i, sannan kuma Gwamnatin ce zata dauki duka hidimar auren da za’a musu sannan za’a sanar da karin bayani kan ranar daura auren.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button