Labarai
Kasar Saudiyya ta soke wajibcin yin allurar cutar Korona kafin shiga Masallatan Harami
Kasar Saudiyya ta soke wajibcin yin allurar cutar Korona kafin shiga Masallatan Harami
Yanzu- yanzu muka sami labarin cewa, Hukumar Hajji da Ummara ta Saudi Arebiya ta sauya wasu sharudda data gindaya wa alhazan gida da na kasashen waje domin yin Ummara.
Advertising
Da ga cikin sharuddan, Hukumar ta soke
wajibcin nuna sakamakon yin allurar cutar korona ta manhajar Tawakkalana kafin alhaji ya shiga cikin Masallatan Harami Guda Biyui.
Wanda Hakan na nufin kafin alhaji ya shiga kasar Saudiya dole zai nuna shedar ya yi allurar cutar korona karo na daya da na biyu.
Sai dai kuma kasar ta soke nuna shaidar yin
rigakafin a matsayin mataki na shiga masallatan Haramin Makka da Madinai.
Advertising
Sannan kuma, kasar ta soke nuna shaidar yin
rigakafin cutar korona kafin maniyyaci ya samu izinin yin Ummara kamar yadda tsarin yake a baya.
Advertising