Yadda aka ci mutuncin jaruma Rukayya Dawayya aka koreta daga gidan haya lokacin da bata da nata
Kamar yadda wasu daga cikin ku suka sani a ‘yan kwanakin nan ne jarumar masana’antar kannywood Rukayya Dawayya ta gina wani katafaren gida wanda zata na rayuwar ta a ciki.
Gidan da jarumar dai ta gina ya dauki hankulan jama’a duba da yadda aka tsara gidan aka kashe masa kudade masu yawa.
Sai kuma muka sami labarin cewa, a baya kafin jarumar ta gina gidan nata sai da ta zauna a gidan haya wanda har aka ci mutuncin ta aka kore ta, ganin hakan ne yasa jarumar tayi yunkurin gina na kan ta domin gudun irin wannan matsalar.
A cikin wani fai-fai bidiyo da muka samu daga tashar “Tsakar gida” dake kan manhajar Youtube munga jarumar tana bada wani labarin dangane da rayuwar ta da kuma zaman da tayi a gidan haya.
zaku iya kallon bidiyon dake kasa domin kuji bayanin da jarumar take fada kan abin da ya faru da ita a gidan haya.
Ga bidiyon a kasa domin ku kalla.