Advertising
Advertising
Labarai

Da dumi Dumi: Kotu ta yanke wa likitan bogi hukuncin sharar titi da bulala 10 a jihar Kano

Kotun Majistare mai lamba 47 dake zamanta a Jihar Kano ta yanke wa wani matashi mai suna Umar Ahmed hukuncin daurin watanni 6, ko sharar titi ta tsawon makonni biyu da kuma bulala goma.

Advertising

Katon ta tuhumi mastashin mai suna Ahmad akan wasu lefuka guda biyu nayin sojan gona da kuma yin cuta.

Kotun ta Zauna a jiya Alhamis, Inda lauyar gwamnati, Asma’u Dalhatu Gwarzo, ta yi umarnin da kotun ta karanto wa wanda a ke zargi laifukan nasa.

Tuni jami’in kotun, Auwal Yakubu Abdullahi ya karanto wa wanda a ke zargin laifukan sa, nan take kuma ya amsa.

Advertising

Tuni Mai Shari’a, Hadiza Muhammad Hassan, ta yanke masa hukuncin wata shida, ko sharar titi na sati biyu da kuma bulala 10.

kotun ta ce sai ya biya Naira dubu 14 ko daurin wata biyu, sakamakon samun sa da laifin karɓar kuɗin wani mara lafiya, bayan ya yi masa ƙaryar cewa shi ma’aikacin lafiya ne a asibitin Nassarawa.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button