Tsohuwar jaruma Safiya Musa ta bayyana cewa kashe Ahmad S Nuhu aka yi ita ma Allah ne ya tseratar da ita
Tsohuwar jaruma Safiya Musa ta bayyana cewa kashe Ahmad S Nuhu aka yi ita ma Allah ne ya tseratar da ita
An dade ana zargin yan film da laifuka da suka shafi bata tarbiyya fidda tsiraici da sauran su amma ba’a fiya zargin su da harkar da ta shafi tsafi ko zubda jini ko wani abu mai kama da haka haka ba sai dai yan kanana kanana zarge zargen asiri a tsakaninsu.
Wani video da muka ci karo da shi a shafin media hausa da suka kwafo daga shafin tiktok na Tsohuwar jaruma a masana’antar Safiya musa, ta bayyana wani sirri da duniya bata sani ba game da mutuwar Jarumi Ahmad S Nuhu inda take bayyana kashe shi aka yi ba mutuwar Allah da Annabi bace duk da dai dama kwanan sa ya kare.
A cikin videon Safiya musa ta bayyana yadda aka basu makudan kudade da zummar zasu je
maiduguri gala Ahmad an bashi 500k ita an bata
700k, inda ganin yawan kudin yasa ita safiya ta karbi dubu ishirin kawai tace bazata jeta ba bayan tafiyar su sai ji tayi Ahmad S Nuhu ya yi Hatsari ya mutu wanda tace da taje dai da ta mutu ko ta sha wahala.
Sai dai a cikin videon bata bayyana wanda take zargi da kashe S nuhun ba bata Kuma bayyana tayi kokarin hanan Ahmad din zuwa ba, kamar yadda a labarin da aka ta aka ce ya mutu bata yi mamaki ba.
koda yake cikin hanzari take bada labarin kuma ana ta kiran ta ana cewa, ta bar maganar jama’a suna jin ta wanda har kiranta aka yi awaya ana ce mata ta bar maganar amma sai da ta kai aya.
Bamu san dalilin da yasa safiya bata fito da wannan maganar ba tsawon shekaru goma sha biyar ba sai yau duk da tasan magana ce da zata iya tada hankali, ko hukuma da yan uwan mamacin suce zasu karkade file su cigaba da bincike wanda dole hakan zai sa a so jin karin bayani daga gare ta.
Akarshe tayi addu’ar Allah ya gyaira industry din in kuma baza ta gyaru ba Allah ya tarwatsa ta tsirarun da suka rage sa gyarata su amfana.
Ga dai bidiyon hirar da aka da tsohuwar jaruma Safiya musa a live dinta na tiktok.