Hukuncin kisa ya hau kan wani mutun sakamakon sace daliba yar shekara 3 a Akwa Ibom.
Babbar Kotu a Uyo, Jihar Akwa Ibom ta yanke wa wani mutum mai shekara 36 mai suna Monday Joshua Okon hukuncin kisa, Biyo bayan garkuwa da wata daliba yar shekara 3 a makarantar Mbierebe Obio da ke Ƙaramar Hukumar Ibesikpo Asutan.
Asirin mutumin mai suna Okon ya tonu ne a kan hanyar sa ta zuwa sayar da yarinyar a Aba, Jihar Abia.
Alkalin kotun, Mai Shari’a Okon Okon ne ya yanke hukuncin a jiya Juma’a bayan ya kama Okon, mazaunin Ekpene Ukpan da ke karamar Hukumar Nsit Ibom da laifin yin garkuwa da yarinyar.
An yanke wa Okon, mai aure da ya’ya 2 hukuncin kisan je tare da wata Cecelia Thompson Ebong wacce a ka yanke mata hukuncin shekara 5 a gidan yari, bayan da ita ce ta taimaka masa wajen sace yarinyar, da kuma riƙe masa ita a cikin babur mai ƙafa uku su ka nufi Aba domin haɗuwa da mai saya da ya ke jiran su.
Ya amsa laifin sa a gaban ƴan sanda cewa ya yi garkuwa da yarinyar ne tun 20 ga watan Yuli, 2018 lokacin a na bikin yaye ɗalibai a makarantar su, inda ya sace da kuma ajiye yarinyar tsawon kwanaki uku a gidansa kafin ya tafi da ita Aba, inda a hanya dubun sa ta cika.
Da ya ke yanke hukuncin, Mai Shari’a Okon ya ce abin takaici ne har yanzu mutane sun ƙi dena ta’adar sata da kasuwancin ɗan’adam, duk da ƙoƙarin gwamnati na daƙile mummunan halin.
Inda ya bada umarnin a rataye Okon har sai ya daina numfashi, ita kuma Cecelia a ɗaure ta shekaru biyar a gidan yari.