Advertising
Advertising
Labarai

Kotu ta yankewa wani Mutun hukuncin kisa dalilin sace wata Daliba mai shekara 3

Kotu ta yankewa wani Mutun hukuncin kisa dalilin sace wata Daliba mai shekara 3

A yanzu haka dai ana yawan kaiwa Dalibai ‘yan makaranta hari domin ayi garkuwa da su a sami kudin fansa, wanda a yanzu haka muka sami labarin cewa wani mutumi ya sace wata Daliba ‘yar shekara uku 3 amma anyi nasarar kama shi.

Advertising

Kamar yadda muka sami labarin cewa, Kotu ta yanke wa wani mutum hukuncin kisa sakamakon sace Daliba yar shekara 3 a Akwa Ibom.

Wata Babbar Kotu a Uyo dake jihar Akwa Ibom ta yanke wa wani mutum dan shekara talatin da shida 36 mai suna “Monday Joshua Okon” hukuncin kisa sakamakon Shin garkuwa da wata Daliba yar shekara uku 3, a makarantar Mbierebe Obio dake Karamar Hukumar Ibesikpo Asutan.

An kama Okon ne a kan hanyar sa ta zuwa sayar da yarinyar a Aba Jihar Abia, Alkalin kotun Mai Shari’a “Okon Okon” shi ne ya yanke hukuncin a jiya Juma’a bayan ya kama Okon, mazaunin Ekpene Ukpan dake Karamar Hukumar Nsit Ibom da laifin yin garkuwa da yarinyar.

Advertising

An yanke wa Okon mai aure da yaya biyu 2 hukuncin kisan ne tare da wata Cecelia Thompson Ebong wacce aka yanke mata hukuncin shekara biyar 5 a gidan yari, bayan da ita ce ta taimaka masa wajen sace yarinyar da kuma rike masa ita a cikin babur mai kafa uku suka nufi Aba domin haduwa da mai saya da ya ke jiran su.

yi garkuwa da yarinyar ne tun 20 ga watan
Yuli 2018 lokacin ana bikin yaye Dalibai a
makarantar su, inda ya sace da kuma ajiye
yarinyar tsawon kwanaki uku a gidansa kafin ya tafi da ita Aba, inda a hanya dubun sa ta cika.

Da yake yanke hukuncin Mai “Shari’a Okon” ya bayyana cewa, abin takaici ne har yanzu mutane sunki dena ta’adar sata da kasuwancin dan Adam, duk da kokarin gwamnati na dakile
mummunan halin.

Inda ya bada umarnin a rataye Okon har sai
ya daina numfashi, ita kuma Cecelia a daure
ta shekaru biyar a gidan yari.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button