Labarai

Likita na ya sanar dani shekara 5 zan kara nabar Duniya sabida cutar da take jiki na, cewar jarumar Nollywood

Likita na ya sanar dani shekara 5 zan kara nabar Duniya sabida cutar da take jiki na, cewar jarumar Nollywood

Jarumar masana’antar fina-finai ta kudancin Nageriya Nollywood mai suna “Kemi Afolabi” ta bayyana cewa, likitanta ya sanar da ita cewa shekara biyar 5 kacal za ta kara yi a duniya ta mutu.

A wata tattaunawa data yi da wani dan jarida mai suna “Chude Jideonwo” jarumar ta ce tana fama da cutar jeji mai suna lupus.

Wanda a cewar ta, likitan yace mata cutar ba ta
warke wa sai dai ai ta shan magani har zuwa
lokacin da Allah ya yi.

Afolabi ta saje bayyana cewa, ta kashe sama da
Naira Miliyan daya 1M a magani amma har yanzu ba ta samu sauki yadda ya kamata ba.

Kamar yadda tace, likitan na ta yanke mata cewa, ki tabbata kullum kina cikin yan uwan ki sabida a kalla zaki iya kara shekar biyar nan
gaba.

Tun a watan Janairu ne Afolabi ta wallafa a
shafinta na kafar instagram cewa, ta rubuta
wasiyya kuma har ta ajiye gurin da za’a binne
ta a makabarta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button