Auren mu ya kasance ne da Mata ta bayan mun hadu a sashen tsokaci na Facebook, cewar wani Matashi
Auren mu ya kasance ne da Mata ta bayan mun hadu a sashen tsokaci na Facebook, cewar wani Matashi
Wani matashi mai suna “Olayede Godwin” ya bada labarin yadda kafar sada zumuntar zamani ta taimaka masa wurin samun matar da ya aura.
Da farko dai hirar ma’auratan ta fara ne a bangaren tsokacin wallafar Legit.ng na kasar sada zumunta Facebook, inda suka fara hirarraki a junan su.
Daga wannan lokacin ne basu kai shekara da sanin juna ba masoyan suka karfafa soyayyar su, sannan sukayi aure a watan Maris din da suke ciki na shekarar 2022.
Matashin mai suna “Oloyede” ya kasance dan Najeriya ne inda a wani sako da ya tura wa Legit.ng ya bayyana yadda ya hadu da matarsa mai suna “Talatu Precious Mohammed Akoa”.
Oloyede ya bayar da labarin yadda ya hadu da matarsa a sashin tsokaci na kafar sada zumunta ta Facebook, karkashin wallafar da shafin Legit.ng ta yi.
Inda Oloyede yake cewa, mun hadu gami da yin aure bayan watanni uku.
Kaddara ta hada su a wajen shagalin bik inda a nan ne suka yimusayar Lamba waya, haka zalika matashin ya turo da tsala-tsalan hotunan da suka dauka na kafin aure “Pree Wedding Picture”.
Oloyede ya yu wata sanarwa cikin wani dan gajeren rubutu ga Legit.ng kamar haka.
A zahirin gaskiya mun hadu a Facebook ne kuma hirar mu ta farko akan wata wallafar da kuka yi ce.
Bazan iya tunawa da wallafar ba bayan watanni uku da muka hadu a wani biki, inda muka yi musayar Lamba.