Advertising
Advertising
Labarai

Bello Muhd Bello ya janyowa kan sa bakaken maganganu bayan kudin da ya bukata a tura masa dan Shehu Inyass

Bello Muhd Bello ya janyowa kan sa bakaken maganganu bayan kudin da ya bukata a tura masa dan Shehu Inyass

Jarumi Bello MuhdBello ya saka kokon barar shi ga masoya Annabi da masoya Shehu Ibrahim Inyass da su cika masa asusun ajiyar sa na banki dan alfarmar shehu ibrahim inyass, inda yawallafa hoton shehun gaminda hadawa da lambar asusun ajiyar tashi sai dai fa ya tabbatarwa da masoyan shehun bashi da wata matsaiar kudin an bashi Kashewa zai yi inda ya rubuta.

Advertising

Ni Bello Muhammad Bello General BMB bani da wata matsala ta kudi, kuma idan an samin kudin zan cinye domin Shehu ne ya bani a cikamin kudi a Account.

Sai dai ko da ganin wannan an yi ta masa tsokaci da rashin kyautawar sa inda kadanne suka goyi bayan sa har wasu na maganganu marasa dadi a gareshi, da ma shehun gaba daya.

Advertising

Ga kadan daga cikin mutanen da suka masa tsoka kan wannan bukata tashi.

Umarmusa718: In har Baka da matsalan Kudin kuma kana ikrarin idan sun baka shehu ne ya baka to me yasa kai baza ka bayar abinda duk kake dashi ba kaima kace musu Shehu ne ya basu. Wanda na tabbatar da yawan wanda zasu tura maka kudin ka fisu wadata dai-dai gwargwado. Allah ya cigaba da ganar damu gaskiya ya bamu ikon binta. #SakiKowa.

Og_graphics_design: Arziqi samu rashi duk daga Allah ne kuma Allah shine yake bayarwa ga wanda yaso wanin ALLAH SAIDAI YAZAMA sila Amma ba wanda yake bayarwa sai Allah plz Adinga sanin abinda za,a furta coz wannan yana CIKIN SHIRKA TA DA,A A CIKIN LITTAFIN KITABUT TAUHIDbangaren Aksamu shirk.

realbalalas70: Shirka! Kaje Shehu na kabari ya baka kudin idan yana da shi….Allah ne mai komai, mai bayar wa kuma mai hanawa.

innawuromuhammad: Mtsssss wlhy yan film din Nan Kuna rainawa kanku arziki Anki Asa kudin kazo ka kwata ko katuro shehu ya kwatarma.

og_graphics_design: Duk lokacin da kwadayi ko kaunar wani abu ya rufe mana ido to mu roka a wajen Allah kuma mu dogara ga Allah wajen yarda da sakamakon samu ko rashi. Duk duniya in da za’a taru mutane da aljanu to basa iya amfanarwa ko cutarwa sai da yardar Allah. Hakika duk wanda ya dogara ga Allah to Allah zai isar masa. Mi kejawo rashin tawakkali, har ana hasarar imani, da rashin yaqini na dogaro ga Allah yayin neman wani abu a rayuwa? Oh.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button