Martanin Bello Muhd Bello ga masu cewa zasu daina bibiyar shafinsa sabida ya roki kudi don Shehu Inyass
Martanin Bello Muhd Bello ga masu cewa zasu daina bibiyar shafinsa sabida ya roki kudi don Shehu Inyass
Kamar yadda wasu suka sani daga cikin ku jarumin masana’antar kannywood General BMB wanda aka safi sani da Bello Muhammad Bello, ya mika kokon barar sa a shafin sa na sada zumunta instagram yana mai cewa a sa masa kudi a asusun sa na banki don Shehu Ibrahim Inyass.
Inda ya wallafa hoton Shehu Inyass tare da cewa, bashi da matsalar kudi koda an bashi ma kashewa zai yi.
Nan take mabiyan shafin nasa suka fara tofa albarkacin bakin su suna nuna rashin jin dadi kan rokon al’umma da yake a saka masa kudi a asusun sa na banki sabida Shehu Inyass.
To a yanzu kuma Bello Muhammad Bello ya bayyana a cikin wata bidiyon yana martani ga wadanda suke cewa zasu yi unfollow na shi, ma’ana subar shafin na sa sabida yana cewa a saka masa kudi don Shehu Ibrahim Inyass.
Zaku iya kallon bidiyon dake kasa domin kuji martanin da yake musu.