Advertising
Advertising
Labarai

Wani mai garkuwa da Mutane ya kai kara gaban kotu domin hana shi kudin fansa da aka yi

Wani mai garkuwa da Mutane ya kai kara gaban kotu domin hana shi kudin fansa da aka yi

Wani dan garkuwa da mutane yaki amincewa da dubu dari biyu N200,000 cikin Naira Miliyan goma sha biyu 12 da aka bashi na kudin fansa, wanda har hakan yasa ya kai rahoto wajan ‘yan sanda.

Advertising

Wani mutum dake jihar Adamawa ya bayyana cewa, shi dan kungiyar masu garkuwa da mutane ne wadanda suka karbi kudinn fansa har Naira Miliyan goma sha biyu 12 daga hannun wasu mutane biyu da aka yi garkuwa da su.

Mutumin mai suna Sadu Bunkawu ya shaidawa ‘yan sanda cewa, ya samu sabani ne da ‘yan kungiyqr tasu masu garkuwa da mutane, bayan sun ba shi Naira dubu dari biyu 200,000 kacal daga cikin Naira Miliyan goma sha biyu 12 da suka samu a aikin da suka yi na karshe, kamar yadda The Nation ta rawaito.

Mutumin ya bayyana kason nasa da cewa, kudin da aka bashi sun yi kadan sai ya kai karar abokan aikin nasa masu garkuwa da mutane ga ‘yan sanda, domin su bi masa hakkinsa na rashin adalcin da aka masa.

Advertising

Bunkawu mai shekaru ashirin da takwas 28 dan kauyen Filingo dake karamar hukumar Jada a jihar Adamawa ya bayyana cewa, an biya su kudin fansa Naira Miliyan goma sha biyu 12 a lokacin da suka yi garkuwa da wasu mutane Umaru Diffiwa da Umaru Babidi ‘yan unguwa daya.

Sannan ya bayyana nadamar sa a kan cewa, lallai aikin ya yi masa illa domin hatta Naira dubu dari biyu 200,000 da ya karba ya fadi a hanyar sa ta komawa gida.

Rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa ta gurfanar da dan garkuwar Sadu Bunkawu a gaban babbar kotun majistare mai lamba daya 1 dake Yola, bisa zargin hada baki da kuma yin garkuwa da mutane.

Lokacin da aka karanta ma sa rahoton bayanin Farko kuma aka fassara masa a gaban kotu, ya amsa laifinsa.

Bayan kammala karar, dan sanda mai shigar da kara ya roki kotun da ta dage shari’ar don ba shi damar kammala bincike tare da kai takardar karar zuwa sashin shari’a, don neman shawarar lauya.

Alkalin kotun mai suna “Muhammad Abdullahi” ya amince da bukatar dage sauraron karar har zuwa saban watan da zai shigo na Afrilu.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button