Yadda wasu Matasa suka hana jami’an tsaro kama wani mai saida Bindugogi a jihar Plateau
A jiya Asabar ne dai al’ummar kauyen Vom da ke lardin Vwang a Karamar Hukumar Jos ta Kudu suka hana sojojin rundunar “Operation Safe Haven” kama wani da ake zargin da kasuwanci da kuma hada bindigogi.
Ishaku Takwa, jami’in yada labarai na rundunar ya bayyana haka a wata sanarwa a jiya Asabar a garin Jos, a cewar Takwa mutanen garin kawai sai suka fito da yawa su ka rika jifan sojojin da
dutsina da sauran su domin su hana a kama
wanda a ke zargin.
Sannan yace, wani bayanin sirri ne rundunar ta samu da ga majiya mai tushe, shi ne dakarun suka hadu suka kai simame da sanyin safiyar
Asabar din domin su cafke wanda a ke zargi.
Takwa ya kara da cewa, duk yunkurin da sojojin suka yi nasu kwantar wa da ‘yan garin hankali bai yiwu ba, inda suka harzika suka rika jifan dakarun da dutsina da makamai masu hadari, inda ya ce jami’an sojin sun nuna kware wa wajen kin tunzuri da hasala.
Jami’in yada labaran yace, domin kada abin ya haifar da da maras idanu sai kwamandan rundunar mai suna “Ibrahim Ali” ya bada umarnin janye sojojin ma gaggawa.
Muna Allah wadai da wannan ta’ada ta hana mu mu kama mai laifi, amma muna masu gargadin al’umma akan matsalar da boye mai laifi zata haifar a cikin al’umma, a cewar Takwa.