Advertising
Advertising
Labarai

Ministan shari’a Abubakar Malami ya wanke Abba Kyari daga zargin karbar cin hanci a gurin Hushpuppi

Ministan shari'a Abubakar Malami ya wanke Abba Kyari daga zargin karbar cin hanci a gurin Hushpuppi

Shahararran marubuci Datti Assalafiy ya wallafa wani dogon bayani a shafin sa na sada zumunta Facebook bayan da aka wanke shi daga zargin karbar cin hanci a wajan Hushpuppi.

Advertising

Datti Assalafiy ya wallafa dogon bayanin kamar haka.

Maigirma Ministan Shari’ah kuma babban Lauyan Gwamnatin Tarayyar Nigeria Dattijon
kirki Abubakar Malami, SAN bayan ya karanci
sakamakon binciken case din Sarkin Yakin
Nigeria DCP Abba Kyari karkashin jagorancin
marigayi DIG Joseph Egbunike akan zargin
karban cin hanci daga Hushpuppi, Ministan
ya mayar wa shugaban ‘yan sanda amsa a
rubuce cikin takarda mai dauke da reference
number kamar haka: DPPA/LA/814/21.

A cikin takardan wanda ya fito daga ofishin
Maigirma Ministan Shari’ah sashin gabatar da kara Department of Public Prosecution
(DPP) wanda sune suke nazarin dukkan kararraki a ofishin Ministan Shari’ah karkashin jagorancin Director of Public Prosecution Barrister Muhammad Abubakar, sunce DCP Abba Kyari bai aikata laifin karban cin hanci daga Hushpuppi ba, don haka bai da wata tuhuma akan wannan shari’ah.

Advertising

An zargi Abba Kyari akan wadannan laifuka kamar haka.

-Crimina| conspiracy

-Aiding and abetting Internet fraud

-Wire fraud

-|dentity Theft

-Money laundering

Sashin gabatar da kara daga Ofishin Maigirma Ministan Shari’ah sunce babu laifi daya da Abba Kyari ya aikata.

Malami ya rubutawa IGP takarda kamar haka.

Ina sanar da kai cewa bayan dogon nazari da lura akan batun shari’ar Abba Kyari da Hushpuppi inda kukace an gano an tura kudi cikin wadannan account number: 2255416115 Zenith Bank mallakin Usman Ibrahim Waziri, 0130665392 Guaranty Trust.

Bank mallakin Adekoye Sikiru, 2080537566 Zenith Bank mallakin Hussein Ala da kuma kudin da aka tura wa wata mata mai suna
Sharon Festus, dukkan kudaden da aka tura cikin account din masu account din sun cire
kudin sunyi amfani dashi, lura da haka wannan bai shafi Abba Kyari ba, babu wata shaida kai tsaye ko shaida karkatacciya data nuna yana da laifi anan, kuma masu account number din su 20 sun bada shaida sun tabbatar basu da wata alaka da Abba Kyari kudin su ne.

A cikin takardan da Ministan Shari’ah ya rubutawa shugaban ‘yan sanda, ya bada shawara wa IGP akan ya tsawatar ko ya hukunta DCP Abba Kyari bisa wasu kura-kurai ko laifuka da yayi guda biyu wanda sukaci karo da dokokin aiki, kuskure na farko shine Abba Kyari ya kama wani mutum ya tsare na tsawon wata guda ba tare da ya kaishi kotu ba.

Sannan sai yunkurin kare kansa da yayi a shafinsa na facebook ba tare da ya karbi umarnin shugaban ‘yan sanda ba Alhamdulillah Jama’a ku tayamu murna sarkin yakin Nigeria yayi nasara akan wannan case din da taron dangin maciya amana da wakilan ‘yan Biyafara suka hadu suka kulla masa, sukace yana da alaka da gawurtaccen dan damfara Hushpuppi domin su huce takaicin kawar da Kwamandojin
yakin Biyafara da yayi bayan sun dawo daga
karban horon soji a Kasar Izraa’ilah.

Insha Allah kamar yadda Sarkin Yaki DCP Abba Kyari yayi nasara akan wannan haka zaiyi nasara akan makircin da aka kulla masa a NDLEA.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button