Advertising
Advertising
Labarai

Obasanjo: Tsoran bulala ne yasa na tsere daga makarantar allo.

Tsohon shugaban kasar Nigeriya Olusegun Obasanjo, ya ce tsoran bulala ne yasa ya tsere daga makarantar allon.

Advertising

Tsohon shugaban kasar ya bayyana cewa tun yana karami yaro aka sanya shi a makarantar allo, wadda ake kira Ile-Kewu a kasar Yarabawa, amma gudun bulala ya hana shi ya zauna a makarantar allon.

kaman yadda nasha fada cewar tsoron dorina ne ya hana na tsaya na iya karatun larabci, kuma har yanzu na kasa mantawa da wasu wake wake da ake mana a wannan lokacin ba, inji shi.

Obasanjo, wanda a yanzu yake da digirin digirgira fannin Tauhidin Kiristanci, ya yi bayanin ne a taron nadin Sheikh Salis Alao Adenekan a matsayin Khalifan Darikar Tijaniyyah na Kasar Yarabawa da jihohin Edo da Delta.

Advertising

A jawabinsa ga taron, Obasanjo, ya bukaci mahalartan da su dage wajen aikata ayyuka na gari domin samun dacewa da shiga Al-Jannah Firdausi.

Ya ce, “Babban manufar rayuwa ita ce samun shiga Al-Jannah, kuma duk wanda ya san darajar Al-janna, ba zai taba sakaci da addini ba a tsawon rayuwarsa.”

Taron dai ya samu halarcin wakilan ’ya’yan Shugaban Darikar Tijjaniya, Sheikh Ibrahim Niass, wadanda Sheikh Abdullah Baye Ibrahim Niass ya jarogranta daga birnin Kaulaha na kasar Senegal; Akwai kuma baki daga jihohin Kudu Maso Yammacin Najeriya da kuma jihohin Edo da Delta.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button