Yan biyun da suka halaka mahaifiyar su nadaga cikin mutun 81 da saudiya ta zartarwa da hukuncin kisan da aka zartar.
Wasu yan tagwaye yaya da suka hakala mahaifiyar su sun kuma yiwa Baban su rauni da kuma dan uwan baban su, Suna daga cikin mutun 81 da saudiya ta yankewa hukuncin kisa.
A watan Yulin shekarar 2016 ne yan biyun suka ja mahaifiyar yar tasu mai shekaru 67 zuwa dakin ajiya (store) inda suka dinga yankar ta da wuka babu kakkautawa.
Bayan mahaifiyartasu, sai suka koma kan Mahaifin su mai shekara 73 wanda yake a wani bangare a cikin gidan, inda shima suka so-soka masa wuka. Bayan sun gama da uban sai suka farwa kanin su mai kimanin shekaru 22 a duniya inda shim suka kai masa kaman yadda sukiwa mahaifin su.
Daga bisani an gano yan biyun nada alaka da kungiya ISSI wanda suke da akidar kafirta kowa. Dalilin dayasa suka halaka mahaifiyar su suka kuma yi yinkurin halaka mahaifin shima sabida bai yadda da mumunar akidar da suke kai ba