Labarai
Yanzu-yanzu Kotu ta dage ranar da za’a dauki mataki kan belin DCP Abba Kyari
A yau Litinin ne Babbar Kotun tarayya dake Abuja ta sanya ranar ashirin da takwas 28 a matsayin ranar da zata yanke kwarya-kwaryan hukunci a kan belin dakataccen Mataimakin Kwamishinan ‘yan Sanda Abba Kyari.
Advertising
Alkalin kotun, Mai Shari’a Emeka Nwite ne ya
sanya ranar bayan ya saurari muhawara
tsakanin lauyan mai kara da wanda ake kara,
Lauyan NDLEA Sunday Joseph ya shaidawa
kotun cewa wanda ake kara na 4 da na 5 basu bada hadin kai ba, inda ya roki kotun data
basu umarnin rubuta takardar rantsuwar yin da’a.
Daga nan ne sai kotun ta bada umarnin a mayar da Abba Kyari da sauran wadanda ake zargi tare da shi zuwa gidan yarin har sai ranar ashirin da takwas 28 ga Maris domin yanke kwarya kwaryan hukunci a kan belin na sa.
Advertising