Advertising
Advertising
Labaran Kannywood

Anzo wajen: Kishi ya hana Aisha Humaira zuwa wajen bikin Bashir Mai Shadda da hasana Muhammad.

A wani bincike da jaridar mu ta gudanar mun gano wasu jarumai da basu halarci bikin Bashir Mai Shadda ba matar tasa Hasana Muhammad, Daga ciki har da Aminiyar Bashir mai Shadda wato Aisha Humaira.

Advertising

Aisha itama tabi sahun wanda basu zo bikin ba kuma jarumar aminiya ce ga Ango idan anyi la’akaci da shakuwar da take tsakanin su.

Daga cikin jarumai hudu da basu halarci bikin ba sun hada da Rahama Sadau, Nafisat Abdullahi, Hadiza Gabon da kuma fati washa sai Aisha Humaira itama data bi sahun wanda basuje ba wanda ake ganin ko kishi ne ya hanata zuwa irin abinda maryam Yahaya taso aikatawa, sanin ku ne dai maryam Yahaya tsohuwar Budirwar mai shadda ce.

Idan zaku iya tunawa kafin bikin Bashir Mai Shadda wasu hotuna sa shida Aisha Humaira suka ringa yawo wanda wasu suke zatan ita zai Aura, Sai daga baya yay bayanin dalilin daukar hoton a shafin sa.

Advertising
Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button