Advertising
Advertising
Labaran Kannywood

Maryam Yahaya tayi wankan kece raini daya dauki hankula ya yin da ake bikin tsohon Saurayin ta Abubakar mai Shadda

Maryam Yahaya tayi wankan kece raini daya dauki hankula ya yin da ake bikin tsohon Saurayin ta Abubakar mai Shadda

Kamar yadda kuka sani jarumar Maryam Yahaya ta kasance tsohuwar Budurwar Furodusa Abubakar Bashir Mai Shadda, inda suka sha soyayyar su a baya.

Advertising

A lokacin da ake shagalin bikin Abubakar Mai Shadda da Hassana Muhammad ta baiwa jama’a mamaki ganin ganin yadda bata nuna wani alamun kishi ba.

Domin Maryam Yahaya ta halarci wajan bikin inda aka shafe tsawon kwanaki ana gudanar da shgulgulan bikin iri-iri, inda jarumar take daukan wanka na kece raini.

Duk wani anko da aka yi a bikin Mai Shadda sai da Maryam Yahaya tayi tare da nuna farin cikin ta, inda tayi ta tikar rawa a wajan bikin da kowa ya yi mamakin hakan.

Advertising

Jarumai da mawaka da sauran mutane ‘yan uwa da abokan arziki sun yi dandazo wajan zuwa bikin inda aka dinga barin nairori.

Manya-manya a masana’antar kannywood irin su Ali Nuhu, Rarara, Adam A. Zango da sauran su, duk sun yi masa kari wanda hakan yasa bikin ya dauki hankali al’umma matuka.

A bangaren manyan mata kamar irin su Saratu Gidado wato Daso, Teema Makamashi, Hadizan Saima da sauran su, duk suma sun halarci bikin hatta tsofaffin jarumai kamar su Fati Bararoji, Masura Isah duk sun je.

Bayyanar Maryam Yahaya wacce tsohuwar Budurwar Abubakar Mai Shadda ce tayi matukar ba mutane mamaki, sabida ba’a yi tunanin zata je ba sabida wasu dalilai.

Tun da aka fara shirye-shiryen bikin mutane suka dinga tsegumi har ta akan cewa, ba’a ga Maryam Yahaya ta wallafa katin gayyata ko kuma ta taya ma’auratan murna ba.

Inda wasu suka dinga tambayar cewa, ko dai kishi ne ya hana ta wallafawa sabida kusan duk wasu ‘yan masana’antar suna ta wallafawa tare da yi musu fatan alheri.

Ana cikin wannan maganganun kwatsam sai ga Maryam Yahaya ta bayyana sanye da ankon bikin cike da murna, inda ta bayyana a wurin shagalin wanda hakan ya yi matukar baiwa jama’ar wajan mamaki.

https://www.instagram.com/p/CbDhrB7NW8x/?utm_medium=copy_link
https://www.instagram.com/p/CbDz-amN9Qv/?utm_medium=copy_link
https://www.instagram.com/p/CbFWIdbtW6N/?utm_medium=copy_link

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button