Advertising
Advertising
Labarai

Matsalar tsaro ta gyaru sosai a Nageriya domin har yanzu ‘yan ta’adda basu kai hari wani wajan ba, Inji Mustapha

Sakaraten Gwamnatin tarayya “SGF” Boss Mustapha ya bayyana cewa, matsalar rashin tsaro dake damun kasar Nageriya ta gyaru sosai, kamar yadda shafin hausaloaded suka ruwaito.

Advertising

Mustapha fadi cewa, matsalar rashin tsaro da tayi katutu a Arewa maso gabashin da kuma barazanar raba kasa da Kudu maso gabas suke ta yi a baya duk sun yi sauki.

Ya bayyana hakan ne ya yin jawabi a wani taro da aka gudanar a garin Kaduna a ranar Alhamis 10 ga watan Maris.

Kamar yadda Mustapha yace, a yanzu haka ‘yan ta’adda sun mika wuya tare da tuba daga munanan ayyukan da suke aikatawa.

Advertising

Sannan Mustapha yace, Rashin tsaro ya gyaru kwarai a fadin kasar nan, barazanar rana kasa da kudu maso gabas da kuma wani yanki na kudu-kudu suke yi ya ragu kwarai.

Mun samu kwanciyar hankali don mun dade bamu samu rahoto akan ‘yan ta’adda sun kai farmaki wani wuri ba.

Rundunar Operation Sharan Daji tare da taimakon jami’an rundunar ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro na sirri sun taimaka wurin ganin bayan ‘yan ta’adda.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button