Advertising
Advertising
Labaran Kannywood

Nan gaba kasan za’a sake shagalin biki a kannywood na jaruma Teema Yola tare da wani Matashi

Ficacciyar jarumar masana’antar kannywood wacce tayi sharafin ta a cikin shirin Labarin mai dogon zango Fatima Isa wacce aka fi sani da Teema Yola, tana shirin yin aure da wani masoyin ta.

Advertising

Mun sami sanarwar ne daga shafin abokiyar sana’ar ta wacce ita ma jaruma ce a masana’antar kannywood Umma Shehu, inda ta wallafa wata gajeriyar bidiyo a shafin ta ma sada zumunta instagram ta Teema Yola tare da masoyin nata wanda zai aure ta.

A ‘yan kwanakin nan dai jaruman kannywood Mata sai aure suke yi lamarin da ya baiwa mutane mamaki, duba da yadda a baya auren bai dame su ba.

A cikin ‘yan watannin nan sai shagalin biki ake a masana’antar ta kannywood wanda zuwa yanzu an daura auren a kalla jarumai hudu 4 da Furodusa daya 1 wato Abubakar Bashir Mai Shadda.

Advertising

An fara daura auren ne a tsakanin wasu jarumai biyu a masana’antar a watan da ya gabata na Faburairun, inda aka daura jaruma Aisha Aliyu Tsamiya da kuma jaruma Hafsat Idris wacce ake wa lakabi da barauniya.

Wanda kuma a yanzu aka daura auren Furodusa Abubakar Bashir Mai Shadda tare da Hassana Muhammad, inda aka daura auren nasu a ramar 13 ga wannan watan da muke ciki na Maris.

To a yanzu kuma mun sami wata sanarwar auren da za’a sake yi a masana’antar kannywood din, inda jaruma Umma Shehu ta wallafa a sanarwar a shafin ta instagram za’a fara shirye-shiryen auren jaruma Teema Yola.

Sai dai Umma Shehu taba sanar da ranar da za’a daura auren Teema Yola ba amma ana ganin kamar ita ce ta gaba akan layi, inda ta wallafa bidiyon Teema Yola tare da wanda zai aure ta.

Ga bidiyon a kasa domin ku kalla.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button