Advertising
Advertising
Labarai

Tsadar man fetur ta sanya ‘yan garuwa sun yi yajin aiki inda mutane suka shiga mawuyacin hali

Tsadar man fetur ta sanya 'yan garuwa sun yi yajin aiki inda mutane suka shiga mawuyacin hali

Al’ummar unguwannin Walawai da Unguwa uku a Karamar Hukumar Tarauni dake Jihar Kano sun wayi garin jiya da matsalar karancin ruwa sakamakon yajin aikin da masu sayar da ruwa, wadanda aka fi sani da yan garuwa a jihar.

Advertising

Daily Nigerian Hausa ta jiyo cewa, yan garuwan sun tafi yajin aikin ne sakamakon wahalar man fetur data sanya masu gidajen ruwa sun kara farashin sabida man fetur ya yi tsada.

A cewar yan garuwan, sun kasance suna sayar da duk jarka daya akan Naira 20, amma sabida karin kudi da masu gidajen ruwa inda suke saro ruwan suka yi musu, shine suma suka kara Naira 10 a kan ko wacce jarka ya zama Naira 30 kenan.

Sai dai kuma yan garuwan sun koka da cewa,
mutanen gari sun ki amincewa da karin farashin, inda suke matsa wa a sayar musu da jarka uku a kan Naira 50.

Advertising

Mu kuma muka ga baza mu iya sayar wa a kan Naira 20 kowacce jarka ba shi ya sa muka ce kawai mu hakura da sayar da ruwan har sai komai ya daidaita, in ji yan ga ruwan.

Bayan haka kuma ba zaku iya sayarwa akan jarka uku Naira 50 ba gara mu zauna mu dena
sayar da ruwan sabida mun fuskanci
al’umma sun ki yarda, sun kasa fahimtar
cewa muma an yi mana karin Naira 20 akan
kowacce kura.

Bello Na Allah Shugaban masu Gidajen ruwa
na yankin yace, yan garuwan basu yi laifi ba da suka tafi yajin aiki sabida al’umma basu fahimci cewa suma an yi musu karin kudi ba.

A cewar Na Allah, suna sarar wa yan garuwan ruwa akan Naira 80 ko wacce baro, amma
sabida tsadar da man fetur ya yi dole an
maida shi Naira 100 akan ko wacce baro.

Ya kara da cewa, masu gidajen ruwa na sayan
galan din man fetur akan Naira 3,600, sabanin a
da ana sayar da shi Naira 1,200.

Ya yi kira ga al’ummar yankin da su fahimci
yanayin da ake ciki, subada hadin kai su rika aiyana ruwan akan Naira 30 a duk jarka, inda ya
ce su suke amfana da ruwan kuma dole ne a yi amfani da shi.

Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa, yan mata ne dai da kananan yara keta yawo da ababan diban ruwa domin neman ruwan da za’a yi amfani da shi a yankin.

Rahotanni ma sun bayyana cewa, mutanen yankin sun fara shiga wani mawuyacin hali inda yara basu samu zuwa makaranta ba sabida ba ruwan da za’a yi musu wanka da karin kumallon safe.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button