Advertising
Advertising
Uncategory

Turkashi: Wani matashin dan adaidaita Sahu yayiwa fasinja karfa-karfa Akan wayar sa.

Wani matuƙin babur mai ƙafa uku, wanda a Jihar Kano a ka fi sani da adaidaita-sahu, mai suna Abdullahi Baba-kura, ya shiga hannun jami’an Hukumar Kula da Tituna ta Jihar Kano, KAROTA bayan da ya sace wa fasinjansa wayar salula.

Advertising

Manema labarai sun jiyo cewa an damke Baba-kura ne kwanaki biyu bayan kotu ta bada belin sa sakamakon aikata laifin ƙwace wayoyi.

Dubun wannan bawan Allah mai suna Baba-kura ta cika ne a ranar Litinin, bayan da ya ɗauki wani fasinja a cikin adai daitan sa, su na tsaka da tafiya, sai ya yaudare shi ya kashe babur ɗin ya kuma ce fasinjar ya taimaka, garin taimakon ne ya zura hannu ya zare masa wayar sa ta hannu.

Bayan fasinjan ya lura ne sai ya kama shi da kokawa, lamarin da ya ja hankalin jami’an KAROTA dake kan titin, inda bayan sun ji ba’asi, sai su ka damƙe shi a kan titin zuwa gidan gwamnati a garin Kano.

Advertising

Da hukumar na tuhumar sa, Baba-kura da bakinsa ya amsa aikata laifin, inda ya ce kwanaki biyu kenan da bada belin sa a kotu.

Da ya ke jawabi a kan lamarin, kakakin KAROTA, Nabilusi Abubakar Ƙofar-Na’isa, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya ce da zarar hukumar ta kammala bincike, za ta miƙa mai laifin ga rundunar ƴan sanda domin gurfanar da shi a kotu dan ya girbi abinda ya shuka.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button