Labarai

Atiku Abubakar ya bayyana cewa Tinubu ya taba masa alkawarin cewa zai masa mataimakin shugaban kasa

Atiku Abubakar ya bayyana cewa Tinubu ya taba masa alkawarin cewa zai masa mataimakin shugaban kasa

Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar ya bayyana cewa, Jagoran APC na Kasa Bola Tinubu ya taba cewa zai yi masa
Mataimaki lokacin da shi Atikun ya tsaya takarar Shugaban Kasa a jam’iyar “ACN”, Atiku ya bayyana hakan ne yayin tattaunawa da Kwamitin Amintattu na “PDP” a Abuja.

A cewar Atiku Abubakar, bai yarda ya baiwa Tinubu mataimakin ba sabida yana son ya dauko wanda zai masa Mataimaki da ga Kudu maso Gabas, inda ya dauko Sanata Ben Obi.

Atiku ya kara da cewa, wasu suna cewa ne a
baiwa Kudu maso Gabas dama gashi kuma
yaki yarda da rokon Tinubu, duk da shi ya baiwa Atiku tikitin takarar ya kuma sanya masa sharudda, amma bai yarda ba yaje ya dauko da ga bangaren na inyamirai.

Sai Atiku yace, Tinubu ba zan dauke ka ba shi ne na dauko Ben Obi, Atiku ya kuma tuna sanda ya kara daukar Mataimaki daga Kudu maso Gabas inda ya dauki Peter Obi a 2019, lokacin da ya tsaya takarar shugaban kasa a jam’iyar PDP.

Daga nan ne sai Atiku yace, bai ga dalilin da yan Kudu maso Gabas zasu ce a basu dama ba, musamman duba da tarihin da ya bayar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button