Advertising
Advertising
Labarai

Hasashen da aka yi ya nuna yakin Yukiren da Rasha zai shafi Talakan Nageriya sabida tsadar kayan masarufi da za’a yi

Yakin Yukiren da Rasha zai shafi Talakan Nageriya sabida tsadar kayan masarufi da za'a shiga nan gaba

Kasashen Rasha da Yukiren sune suke samar da kashi talatin 30 na alkamar da duniya take bukata, da kuma kashi ashirin 20 na masarar da
duniya ke amfani da ita.

Advertising

Hukumar Kula da Abinci ta Amurka ta yi kiyasin a banar nan kasar Yukiren ba zata samar wa duniya da alkama kusan metric ton Miliyan bakwai ba, wanann ba karamin adadi ba ne haka nan ita kanta kasar Yukiren din ta hana fitar da duk wata alkama, acca, da shanu zuwa kasashen waje a dalilin wannan mamaya.

Kasar Rasha kawai a shekarar 2020 ta sayar wa da kasashen Afrika kayan abinci na kusa da Dalar Amurka Miliyan uku 3, wanda kashi arba’in da takwas 48 cikin dari duk alkama ce.

Haka nan kasar Amurka ita ce ta fi kowace kasa sayen kayan abinci don tallafa wa wuraren dake fama da rikici da annobar yunwa a duniya, sannan kuma rabin irin abincin da take saye tana saya ne daga Rasha da Yukiren kenan sabida wannan yaki dole ta juya akalar cinikinta zuwa wasu kasashen domin sayen kayan abincin, wanda hakan zai kara tsauwala tashin farashin abinci a duniya.

Advertising

Talakan Nijeriya zai fuskanci karin farashin biredi, fulawa da taliya a dalilin abin da muka
zayyano a sama, wannan ya biyo bayan dogaro da kasar nan ta yi kacokan akan shigowa da alkama daga kasashen Turai.

Idan muka dubi bangaren samar da takin zamani kuwa, kasar Rasha ita ce kasar data fi kowace kasa samar da sinadaren da ake hada takin zamani, Hakika dalilin wannan yaki farashin takin zamani zai yi matukar tsada a duniya wanda haka yana nufin tsadar kayan amfanin gona ke nan.

Wannan ba zai bar Nijeriya a baya ba wajen
fuskantar hauhawar farashin kayan da ake
nomawa, wannan kuma yana zuwa ne bayan
karin farashin da ake fama da shi sabida zuwan cutar korona data addabi duniya.

Farashin man fetur, man dizal da iskar gas ya fara tashin gwauron zabi, wanda a yanzu gangar gurbataccen mai ta kai Dala dari da talatin da tara 139 a duniya, inda farashin iskar gas ya riga ya ninka kudinsa abin da wannan yake nufi shi
ne da ace mu muke tace man da muke amfani da shi da sai mu ce lallai talaka zai sha jar miya, domin kasar zata sami kudaden shiga masu yawa.

Amma kash tunda sayo tataccen mai muke a kasashen waje dole a sayo da tsada sannan a biya kudin tallafi da tsada, ma’ana dai mu ba zamu ga alfanun tsadar man a duniya ba.

Hasali ma ya kara tsada sabida ba lallai gwamnati ta jure biyan kudin tallafin ba, yadda abin zai shafi talaka shi ne karin kudin sufuri zai kara wa kayan masarufi kudi.

Kamfanoni kuma zasu kara kudin hajarsu sabida suna sayen man dizal da tsada domin sarrafa injinan su, Kasar Misra ta tanadi alkama ga kamfanoninta na wajen watanni takwas masu zuwa domin a cike gibin karancin alkama da zata samu sabida wannan bala’i da aka shiga.

Kuma duk da haka ta hana fitar da taliyar da take sarrafa wa zuwa kasashen ketare domin talakawanta su wadatu da abinci a wannan shekarar, amma mu Shugabannimu sun shagaltu da batun zaben shekarar 2023 basu dauki wani mataki domin saukaka wa talaka
radadin da ake tsammanin zai tsunduma a ciki na tsadar kayan masarufi Sabida ciki na tsadar kayan masarufi sabida wannan yaki na Rasha da Yukiren ba.

Hatta Majalisar Dinkin Duniya ta ce yakin
Yukiren da Rasha zai haifar da bala’in yunwa a duniya, ke nan fatanmu shine Allah ya kawo karshen yakin nan cikin kankanin lokaci ya kuma kare al’umma shiga mawuyacin hali.

Rahoton Daily Nigerian Hausa.

Advertising

One Comment

  1. Ni Iganin Idangwamnatin tarayyar Nigeria bazata Iyafarfadoda matatun man feturdinta gamidakirkiro sabbiba to kawaitasayardasuga yankasuwa domin tayardasu kaga sai ahutada asaran biyan maaikatan bataredasuna aikiba

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button