Advertising
Advertising
Labarai

Na yafewa Nafisa Ishak cin mutuncin data min akan nayi magana kan farjin Mata, inji Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa

Na yafewa Nafisa Ishak cin mutuncin data min akan nayi magana kan farjin Mata, inji Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa

Kamar yadda kuka sani dai jarumar kannywood Nafisa Ishak tayi martani ga Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa bayan wasu maganganu da ya yi akan farjin Mata inda yake cewa.

Advertising

Babu abu mafi muni da kazanta a jikin mace kamar farjin ta, domin tanan suke haihuwa, jinin al’ada.

Inda ita kuma bayan wannan maganar tasa ta maida masa da martani, to sai dai a yanzu jidan jaridar VOA Hausa sun yi shira da Sheikh Aminu Daurawa inda yake cewa ya yafewa Nafisa Ishak kan abin da ta masa.

Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya fara da cewa, Ban so nayi magana ba akan wannan matsalar ina ganin ta wuce, to amma abubuwa guda uku ne zai sa dole nayi magana akai kamar yadda yan uwa suka bukata nayi magana.

Advertising

Abu Na farko: A cikin karatuna babu inda nayi batsa kuma babu inda aka ci zarafin kowa karatu ne akan duniya malamai in suna so su fadakar da mutane, illa duniya da take hallaka da mutane da zubba da jini da ta’addanci da kashe kashe da kidnaping da kashe yara duk anayi ne sabida duniya.

To shine malamai suke fadakar da mutane yadda ake waɗannan ta’addanci duk akan duniya ne saboda Sayyidina Ali R.A shine yayi wannan bayyani shiyasa ni kuma na dauko a cikin wannan tafsiri na Qurtubi

Kuma duk malamai sun gani cikin tafsirin a cikin suratul hadid.

Sayyidina Ali (RA) ne ya fadi. Ga maganar tasa kamar yadda Sheikh ya fade ta kwabo da kwabo:
قال علي لعمار: “لا تحزن على الدنيا فإنّ الدنيا ستة أشياء : مأكول ومشروب وملبوس ومشموم ومركوب ومنكوح ، فأحسن طعامها العسل وهو بزقة ذبابة ، وأكثر شرابها الماء ويستوي فيه جميع الحيوان ، وأفضل ملبوسها الديباج وهو نسج دودة ، وأفضل مشمومها المسك وهو دم فأرة ، وأفضل المركوب الفرس وعليها تقتل الرجال ، وأما المنكوح فهو النساء وهو مبال في مبال، والله إنّ المرأة لتزين أحسنها فيراد منها أقبحها”. انتهى
تفسير القرطبي – القرطبي – ج ١٧ – الصفحة ٢٥٥
Imamul Qurtubi a cikin tafairinsa (17/255) ya ce: Sayyidina Ali ya ce ma Ammar (RA): “Kada ka samu damuwa akan abin duniya domin jin dadin duniya abu shida ne kawai: Abin ci, da na sha, da na sa wa. Sai kuma abin shaka (turare/kamshi) da abin hawa da na aure. To, shi dai abincin duniya mafi dadinsa shi ne Zuma wacce fitsarin kuda ce. Mafi kyan abin sha ruwa ne wanda ko dabbobi shi suke sha. Tufafi kuma duk ba su kai darajar alhariri ba; sakar tsutsa ce. Kamshin turare kuma yana a bayan Miski; jinin wata bera ne. Abin hawa mafi daraja shi ne doki wanda a kan sa ake kisan maza. Aure kuma jin dadinsa yana wajen mata; wurin fitsari ne yake haduwa da wurin fitsari irin sa. Wallahi duk adon da ka ga macce ta yi, inda ya fi munin ne ake bukata (Farji)”.
Tafsirin Qurtubi (17/255).

Malamin yace, Sabida haka ba batsa bane, ba cin fuska bane, ba cin zarafin wani bane, manya manyan malamai na duniya duk sun kawo a cikin litattafansu.

Abu Na Biyu : Da ake gayamin bidiyo yana ta yawo wata ta zageni kamar yadda mutane suka gayamin amma daga baya ta bada hakuri to ni kafin ma ta bada hakurin ni na yafe mata.

Sabida ni mai wa’azi nasan akwai suka akwai yabo akwai zagi sama da shekara talatin 30 naji kalmomi masu dadi naji marasa dadi basa damuna.

Muna godiya ga mutane da kowa ya nuna damuwasa akan abinda ya faru, amma bamu yadda da dauka doka a hannu ba, muna tafan Allah ya shiryar damu ya bamu lafiya da kasar mu lafiya.

Advertising

One Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button