Labaran Kannywood
Sakon Abubakar Mai Shadda ga jaruman kannywood da mutanen suka masa fatan alkairi kan auren sa
Furodusan masana’antar kannywood Abubakar Bashir Mai Shadda wanda a yanzu haka ango ne ga Hassana Muhammad, ya yiwa jaruman kannywood tare da sauran al’ummar da suka masa addu’a ta fatan alkairi kan auren sa godiya ta musamman.
Advertising
A cikin wata bidiyo da muka samu daga tashar “Dalatop24” dake kan manhajar Youtube munga Abubakar Mai Shadda ya bayyana a cikin bidiyon yana mika godiyar sa ga abokan saan’ar sa na kannywood da ‘yan uwa da abokan arziki, duba da yadda aka yi dandanzo wajan halartar auren sa.
Zaku iya kallon bidiyon dake kasa domin kuji cikekken sakon godiyar da Abubakar Mai Shadda yake mikawa ga jaruman kannywood da kuma sauran al’umma.
Ga bidiyon nan a kasa domin ku kalla.
Advertising
Advertising