Wani karamin yaro dan shekaru 3 ya kashe Mahaifiyar sa da Bindiga bisa tsautsayi
Wani karamin yaro mai shekaru uku 3 ya hallaka mahaifiyar sa bisa kuskure a lokacin da yake wasa da wata bindiga, lamarin ya faru ne a birnin Chicago dake kasar Amurka, kamar yadda shafin Hausaloaded suka ruwaito.
Lamarin ya faru ne a ranar Asabat da misalin karfe 8:30 na dare a wajan da ake ajiyar Motoci a wani babban shago, kamar yadda ‘yan sandan gundumar Dalton suka bayyana.
Kamar yadda sanarwar ta ce, kamarin yaron na zaune ne a kujerar baya a cikin motar mahaifinsa inda mahaifin nasa na zaune a kujerar direba tare da mahaifiyarsa a gaban motar.
Ba’a san yadda aka yi yaron ya iya fito da bindigar ba, amma rahotanni sun bayyana cewa ya rika yin wasa da ita ne a kujerar bayan motar.
Daga baya sai ya latsa kunamar bindigar kuma nan take harsashi ya fito ya shiga ta wuyan mahaifiyarsa mai suna “Deejah Bennett” inda ya kashe ta.
BBC ta ruwaito cewa, ’yan sandan Dolton sun ruga da matar zuwa Cibiyar Lafiya ta Jami’ar, sai dai da isarsu likitoci suka tabbatar da cewa ta riga ta cika.
A yanzu haka dai ana tuhumar mahaifin yaron kan mallakar bindigar bisa wannan tsautsayi da ya auku a Kudancin Dolton.