Labarai

‘Yan gunkiyar ISWAP sun yi garkuwa da ma’aikacin lafiya a jihar Borno

A yau Laraba ne Gwamnatin jihar Borno ta
tabbatar da cewa, yan kungiyar ISWAP sun sace wani ma’aikacin lafiya dake aiki a babban asibitin Gubio.

A daren Larabar, da misalin karfe 2:30 na safe ne dai ‘yan kungiyar ISWAP din suka kai hari a
Gubio, inda suka yi awon gaba da kayan abinci da man fetur a motar kai agaji.

Kwamishiniyar Lafiya ta jihar ta bayyana cewa, tabbatar da afkuwar lamarin ga Kamfanin Daillancin Labarai na Kasa “NAN” inda tace lamarin abin takaici ne.

A cewar ta, ma’aikacin lafiyar da aka dauke na daya da ga cikin jajurtattun da suka rage suna aikin duk da hadarin dake ciki.

Sannan ta kara da cewa, ma’aikatar lafiya zata sanarwar hukumomin da suke da ruwa da tsaki a rubuce kamar su rundunar “Operation Hadin
Kai”.

Kwamishiniyar ta kuma yi fatan Ubangiji yasa a sake shi salin-alin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button