Advertising
Advertising
Labarai

Majalisa tarayya naso a fara bawa masu First Class Aiki da zarar sun gama Digiri.

Yan Majalisan tarayya ta Najeriya ta yi kira ga hukumomi da ma’aikatun Gwamnatin Tarayya da su fara bayar da ayyukan yi kai tsaye ga duk dalibin da ya kammala karatun digiri da shaidar karatu mai daraja ta farko (first class).

Advertising

Bukatar hakan ta biyo bayan wani kuduri da dan majalisar, Chinedu Emeka ya gabatar a gabanta ranar Laraba, inda ya ce jami’o’i na samar da daruruwan matasa masu first class din a kowace shekara wadanda suke shan wahala wajen samun ayyuka.

Ya kara da cewa lamarin ya sa matasan da dama yin tururuwa wajen barin kasar nan, inda suke barin masu sakamako mara kyau, wadanda ke da hanyoyi wajen samun aiki, inda ya ce hakan na matukar yi wa kasar illa.

Ya ce matukar kasar ba ta samo hanyoyin saka wa zakakuran matasa ba, za ta jima tana zaune a matsayin koma baya a koda yaushe.

Advertising

Majalisar ta rayya ta kuma bukaci Ma’aikatar Ilimi da ta hada gwiwa da sauran hukumomin gwamnati don tabbatar da an sama wa matasan kasar mafita.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button