Uncategory

Maryam Yahaya: Babu abin da natsana kamar mutuwa bana kaunar ta

Cikin wani shiri na gidan jaridar BBC Hausa wanda suke gayyatar jarumai daga masana’antar Kannywood domin suzo ayi hira dasu, inda a wannan makon ansamu bakoncin jaruma Maryam Yahaya.

Cikin hirar anyiwa jarumar wata tambaya cewar, meyake sakata bakin ciki inda jarumar tabada amsa da cewar ranar mutuwarta tace idan ta tuna ranar dazata mutu takoma ga mahaliccinta takanji bakin ciki.

Saidai wannan amsar da jarumar tabayar ya matukar janyo cece kuce a kafofin sada zumunta domin kuwa mutane sunata fassara wannan maganar izuwa wani abu nadaban, inda suke fadin lallai jarumar tana tsoron haduwarta da ubangiji akan wani zunubi datake aikatawa kenan.

ku cigaba da bibiyar mu dan samun zafafan labarai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button