Advertising
Advertising
Labarai

Wata sabuwa: An sace kudin sadaki ana tsaka da daurin aure a jihar Kano

Wata sabuwa: An sace kudin sadaki ana tsaka da daurin aure a jihar Kano

A wani labari da muka samu mai cike da abin mamaki yadda aka sace kudin sadaki ana tsaka da daurin auren a jihar Kano.

Advertising

Shafin Hausaloaded sun wallafa labarin kamar haka.

A jiya laraba ne 16/03/2022 akaje daura aure daga garin Igabi na jihar Kaduna, zuwa Kano kamar yadda rahotonnu ke tabbatar mana da hakan, “Inda aka nemi sadaki sama ko kasa ba’a Ganshiba.

Sakamakon hakan yasa aka bata lokaci ba’a daura auren ba ana ta kallon kallo a tsakanin juna, Amma daga bisani aka gani a cikin babban rigan daya daga cikin waliyan amarya, inda yace shi bai ma San yadda akayi kudin suka zo jikinshi ba anan dai aka kori waliyin zuwa waje. Inda aka Kira kanin shi da yazama cikon waliyyan amaryan.

Advertising

Wannan lamari ya farune a kano a wata unguwa da ake kira da kurna.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button