Abubakar Malami Ministan Shari’a ya bayyana cewa bazai ajiye mukamin sa ba
Antoni Janar na kasa Ministan Shari’a Abubakar Malami a ranar Alhamis ya bayyana cewa, bazai ajiye mukamin sa ba, kamar yadda Malami yace sai yaga karshen wa’adin mulkin sa a watan Mayu na Shekarar 2023.
Abubakar Malami ya bayyana haka ne a lokacin da yake bada jawabin budewa a wani taro da kungiyar Ma’aikatan Shari’a suka shirya, Kamar yadda shafin Hausaloaded suka ruwaito.
Mutane da dama da suka dogara ga jin bayanai na karyasuna cewa, Abubakar Malami ya ajiye mukamin sa a Matsayin Antoni Janar, kuma Ministan Shari’a ana ganin sa a ofishin sa yana gudanar da aikace-aikace ciki harda halartar taron Majalisar Zartaswa ta kasa a jiya, kuma yanzu yana bude taro a matsayin Antoni-Janar na Kasa.
Abubakar Malami ya cigaba da cewa, akwai karshen komai wa’adina na Mulki har yanzu bai kare ba, ina fatan nayi kyakkyawan karshe.
Jita-jita na cigaba da yawo cewa, Abubakar Malami zaiyi takarar Kujerar Gwamnan jihar Kebbi a Shekarar 2023, amma dan Shekaru 54 bai bayyana ra’ayin sa ba akan haka.